Gwamnatin Jihar Kebbi da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), sun gudanar da bikin ranar yara ta duniya tare da yin kira ga yaran su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi, tashe-tashen hankula, da dabi’un marasa kyau.
Bikin wanda aka gudanar a Birnin Kebbi a ranar Laraba, wani kokari ne na hadin guiwa da AGILE da kungiyar masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke yekuwa kan ilimi.
Bikin ya samu halartar makarantun sakandire guda 10 da suka halarci tarukan kacici-kacici da muhawara a wajen taron bikin.
Babban sakataren ma’aikatar yada labarai da al’adu, Alhaji Buhari Wara, ya nanata kudirin gwamnatin jihar na tallafa wa rayuwar yara ta hanyar ingantaccen ilimi da yanayin Karatu mai kyau.
Ya kuma jaddada cewa jihar na da burin samar wa yara damar samun ilimi mai inganci, kiwon lafiya, tsaftataccen ruwan sha, da muhalli mai kyau.
Hakazalika Alhaji Buhari Wara, ya bukaci yara su mayar da hankali kan karatunsu, su nisanci munanan dabi’u, su tabbatar da tsaron lafiyarsu.
“Yara su ne kashin bayan al’umma,” in ji Wara.
“Yayin da kuka girma, za ku fuskanci kalubale da yawa.
“Ku guje wa shaye-shayen kwayoyi, tashin hankali, da halayen da ba a so, yayin da suke haifar da mummunan sakamako.
“Saboda haka ku mayar da hankali kan karatunku, kuma za ku samu ikon zabar makomarku kuma ku samu hikima.”
Dokta Sahail Sheikh, wakilin UNICEF, ya jaddada sadaukarwar kungiyar wajen yi wa mata da yara hidima, tare da ba su damarmaki a fannoni daban-daban na rayuwa, da suka hada da kiwon lafiya, ilimi, tsaftataccen ruwan sha, hakkin yara, da kariya daga cututtuka masu yaduwa.
Ko’odinetan NYSC reshen Jihar Kebbi, Alhaji Bala Dabo, ya yaba wa Kungiyar UNICEF da Kungiyar CDS ta ilimi bisa shirya gasar kacici-kacici a tsakanin makarantu tare da hadin gwiwar UNICEF.
Kwalejin ‘yan mata da ke Makerar Gwandu ce ta zo na daya a gasar kacici-kacici da maki 60, sai Kwalejin Rayhaan da maki 55, sai makarantar Royal Lead academy da maki 40.
Taken ranar yara ta duniya na bana, “Kyakkyawan Ilimi Yana da Muhimmanci ga Al’umma,” a duk lokacin da aka gudanar da taron, dukkanin makarantun da suka halarci bikin ana ba su takardar shaidar halartar bikin.