Matar shugabar rundunar sojojin Nijeriya, Misis Salamatu Yahaya, ta nemi matan sojojin Nijeriya su taimaka wajen karfafa wa mazajensu wurin yakin da suke yi da ‘yan bindiga a sassan kasar nan.na
Misis Salamatu wadda kuma ita ce shugabar kungiyar matan sojojin Nijeriya, ta bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin da take kaddamar da makarantar da kafa a garin Inugu.
- ISWAP Ce Ta Kai Wa Sojoji Hari A Dutsen Zuma – Rahoto
- Sojoji 2 Da Farar Hula 1 Sun Mutum A Wani Hatsarin Mota A Legas
Ta kuma kaddamar da shalkwatar kungiyar da aka sake yi wa kwaskwarima tare da bayar da tallafin kayan aiki ga asibitin rundunar ta 82 da ke Inugu.
Ta kara da cewa, wannan shawarar ta zama dole saboda muhimmancinsu ga rayuwar mazajen nasu a bangariori da dama.
Salamatu ta bayyana cewa, ya kamata matan su tabbatar da harkokin gidajensu na tafiya yadda yakamata don hankalin mazajen nasu ya kwanta a halin da suke fafatawa da ‘yan ta’adda a sassaan Nijeriya.
Tunda farko, matar shugaban runduna ta 82, Misis Mariya Lagbaja, ta godewa shugabar ta NAOWA a kan dukkan goyon bayan da take bayarwa wajen bunkasa kungiyar.