• English
  • Business News
Sunday, August 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙone-ƙonen Da Ƴan Ta’adda Ke Yi Zai Ƙara Haifar Da Ƙarancin Abinci

by Idris Aliyu Daudawa and Jibrin Baba Ndace
9 months ago
in Labarai
0
Ƙone-ƙonen Da Ƴan Ta’adda Ke Yi Zai Ƙara Haifar Da Ƙarancin Abinci
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Al’amarin yadda ‘yan ta’adda suke cin karensu babu ko babbaka abin yana da matukar daure kai domin kuwa suna yin abubuwan da suka ga dama, su kashe manoma, su kona gonakinsu, ko su kwashe  masu kayan amfanin gonarsu, kai sai dai abinda suka ga damar yi. Yanzu dai ba karamar illa ko matsala suke bada gudunmawa ba ta wajen karancin abinci.

Gaba dayan Jihohin Arewa kadan ba su fusknatar irin wannan halin in ma da akwi su, sai dai kawai ace irin cin fuskar da suke yi a wadancan wuraren sun sha bamban dana wadansu wurare sai daia yi fatan Allah ya taiamaka mana wajen kawo karshen ta’asar da suke yi, da a karshe take samar da karancin abinci.

  • Yanayin Cin Abinci Da Baccin Annabi Muhammadu (SAW)
  • Gwamnatin Bauchi Ta Kaddamar Da Kwamitin Adana Kayan Abinci

Ta irin hakan ne yanzu an samu dalilai da suka sa aka kona gonakin masara na wasu al’umma a karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, barnar da ‘yan ta’adda ne suka yi ta.

Shugaban  kungiyar ci gaban masarautar Birnin-Gwari  (BEPU), Ishak Usman Kasai, wanda kuma har ila yau shine shugaban kungiyar al’ummomin da suke bakin iyaka, a hirar da yayi da manema labarai ya bayyana cewa da akwai wani  abinda ya faru wanda ya shafi yarjejeniyar da aka yi ta zaman lafiya.

Kamar yadda yace, “Wurin da jamia’an tsaro suka kawo zaman lafiya a kokarin da suke yi shine babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.Amma idan ana maganar kauyuka ne babu wani abinda aka yi a wuraren da za ‘a iya cewa sun taimaka hare- haren sun ja da baya.

Labarai Masu Nasaba

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

“Dan haka abinda ya far ranar Lahadi ta makon daya gabata inda wasu ‘yan ta’adda suka kona wasu gonaki kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, shine wasu wurare kusa da Kwoga, Zoko da kuma Gayam. Wurin da akwai wani azabibin shugaban’ dan ta’adda wanda ake kira da suna Yellow Janbros.

“Akwai wani jami’in soja a wurin wanda yana  yin duk abubuwan da suka kamata domin ya samu hanyar gamawa da ‘yan ta’addar wadanda suke bi ta hanyar shanu  zuwa Zamfara, ta Birnin Gwari zuwa Jihar Neja domin kawai su je su kai hare- hare.

Jami’in soja shi da tawagar ta sa sun samu gamawa da wasu ‘yan kungiyar Yellow Janbros. Mako biyu da suka wuce, jami’in sojan ya jagoranci tawagarsa inada suka kai samame lokacin da ‘yan ta’addar suke wucewa daga Neja domin su shiga Birnin Gwari.

“Sanadiyar abinda sojojin suka yi masu ne yasa suka saw a gonakin masarar wuta ranar Lahadi kusa da wurin. Sun yi hakan ne inda suka fadawa mutanen da suke wurin, su zo su sake yin wata yarjejeniyar zaman lafiya, ko kuma su ci gaba da kai masu hare- hare.Da suka ji hakan ne fa sai su al’ummar wurin suka fara tunanin hanyoyin da za su taimakawa jami’an soja su gama da ‘yan ta’adda.

“Maganar gaskiya abinda ya kawo tsaikon rashiun zaman lafiya ya fara ne tun arangamar da suka yi da soja suka yi masu luguden wuta, da lalacewar yarjejeniyar zaman lafiya ta sa su ‘yan ta’addar suka zafafa kai hare- hare a gonakin manoma”.

Kafin dai akai harin na ranar Lahadi, “akwai wani Malamin addini daga sashen Bauchi da Gombe, da ake kiransa Azadu Sunnah, wanda ya zo Birnin Gwari ranar Asabar saboda a samu ayi lamarin daya shafi  yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan ta’adda da mutanen garin, amma kuma ranar Lahadi sai su ka kai wa mutanen wuriin hari.

“Idan ko muddin dai ana bukatar garin Birnin Gwari da gaba dayan sashen Arewa maso yamma su samu zaman lafiya, kamata yayi gwamnati ta tura sojoji zuwa dajin Kuduru, tsakanin Chikun da Birnin Gwari, a tura soja zuwa dajin Kamuku da dajin Kuyanbana  tsakanin  Dan Sadau a Jihar Zamfara da Kaduna , aje dajin Kuzamani akan iyaka Kaduna da Neja”.

Sai dai kuma a dukkan wuraren nkamar yadda ya jaddada, “A dukkan wuraren akwai kungiya- kungiya ta ‘yan ta’adda wadanda suka kai muatane zuwa dazuzzukan,  ga shi kuma babu isassun jami’an tsaro a wuraren da suke da hatsari. Don haka akwai bukatar a shirya rundunar tsaro ta hadin gwiwa tskanin Jiha da Jiha a Jihohin, Kaduna, Neja da Zamfara.Abinda ya kamata ayi ke nan ba kawai a tsaya kan hanya ba ko kuma wasu wuraren al’umma .

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Abinci
ShareTweetSendShare
Previous Post

Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (2)

Next Post

GORON JUMA’A 22/11/2024

Related

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya
Ra'ayi Riga

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

2 hours ago
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas
Labarai

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

5 hours ago
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa
Labarai

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi

6 hours ago
Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP
Manyan Labarai

Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP

9 hours ago
NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru
Manyan Labarai

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

21 hours ago
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu
Ilimi

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

1 day ago
Next Post
GORON JUMA’A 22/11/2024

GORON JUMA'A 22/11/2024

LABARAI MASU NASABA

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

August 24, 2025
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi

August 24, 2025
Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP

Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP

August 24, 2025
Trump Ya Ce Zai Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganawa Da Putin Da Zelensky Lokaci Guda

Trump Ya Ce Zai Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganawa Da Putin Da Zelensky Lokaci Guda

August 24, 2025
Fabio Na Brazil Ya Kafa Sabon Tarihi A Kwallon Kafa

Fabio Na Brazil Ya Kafa Sabon Tarihi A Kwallon Kafa

August 24, 2025
Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

August 24, 2025
NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.