Masu ruwa da tsaki ta bangaren ilimi sun yi kira da a dauki tsari na gaggawa saboda arage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da makarantu masu zaman kansiu.
Yomi Otubela ita ce shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu ta kasa ya yi jawabi ne kan irin tabarbarewar tattalin arziki wanda dalilin hakan makarantu masu zaman kansu suna ji a jikinsu.
- Kamfanin Hakar Uranium Na Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Na’urori Ga Wata Makaranta A Namibia
- An Kama Dillalin Safarar Makamai Dan Aljeria A Zamfara
A hirar da tayi da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar lahadi, ya ce akwai bukatar da dauki tsare- tsare ba tare da bata lokaci ba, wadanda za s taimaka wajen saukaka kudin kayan karatu.
Otubela ya kara da cewar su tsare- tsaren ya dace su samar da wasu hanyoyi da za’a bar daukar haraji akan kudaden bashin da ake ba mabobin kungiyar.
Shugaban na kungiyar NAPPS yayi kira da hadin kai domin samun dama ta lamarin daya shafi fasaha.
Ya ci gaba da bayanin“Mun san cewa idan har aka samu tallafi daga gwamnatoci wadanda za’a ba makarantu masu zaman kansu,hakan zai sa su makarantu masu zaman kansu su rage fiye da yara milyan 18 wadanda basu zuwa makaranta a Nijeriya.”
Otubela ya kara jaddada cewa makarant da yawa karkashin kungiyar sun bullo da tsari na biyan kudin makaranta,inda take aiki tare da Iyayen yara, domin a tabbatar da cewa babu wani yaron da aka bari saboda Iyayen shin a fuskantar matsalolin da suka shafi kudi.
Kamar yadda yayi karin haske kungiyar NAPPS tana yin iyakar kokarinta wajen samar da ilimi mai nagarta, da kuma sanin irin halin rayuwar da al’umma suke ciki, wajen bin lamarin hanyar data kamata.
“Muna fatan gwamnati zata kara kudaden taimakon da take badawa kan tsarie- tsaren horar da Malaman makaranta, da kuma sauran wasu nau’oin taimakon da ake badawa na kudade ga makarantu domin su inganta abubuwan more rayuwa a makarantu kamar yadda Otubela ya bayyana”.
“Hadin gwiwar ba wai abin zai tsaya bane kan taimakon matsalolin da makarantu masu zaman kansu ke fuskanta ba ne, har ma da tabbatar da kowane dalibin Nijeriya ba tare da la’akari yadda mahaifansa suke ba,ya samu ilimi mai nagarta.”
Segun Olayode wanda yana daya daga cikin Iyaye wanda shi masani ne kan kimiyyar data shafi lamarin kula da lafiya, cewa yayi ya kara kaimi ne domin ya biya karin kudin makarantar da aka yi na ‘ya’yan shi.
Wata mahaifiya ma wato, Tolani Odofin, wadda ita ma’aikaciyar gwamnati ce, tace ba zata iya biyan karin kudin makarantar ba, sai dai za ta mai da ‘ya;yanta wata makaranta.
Ta ce “Hukumar makarantar ta rubuta masu takarda lokacin huru inda aka bayyana masu lamarin tabarbarewar tattalin arziki ne yasa aka yik arun kudin makarantar”.
Ta ce “Ni da mijina mun yanke shawarar sa su a wata makaranta saboda ba za mu iya biyan sabon kudin makaranatar.Daga Naira 65,500 zuwa Naira 95,500, bayan haka kuma ga kudin littattafai da sauran kayan karatu sun karu”.