Gwamnatin tarayya na hasashen samun kudin shiga na naira tiriliyan 34.8 a kudirin kasafin kudin 2025. Kudirin ya kuma tsara dabarun sake fasalin bashi da nufin ‘yantar da kudade don ci gaban ababen more rayuwa.
Wannan tsarin yana daya daga cikin muhimman abubuwan da aka tsara na 2025-2027, matsakaaicin dubarun harkokin kudade, wanda majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shi a ranar Alhamis.
- Gwamnati Ta ÆŠage Haramcin Tura Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Bankuna Da Sauran Masana’antuÂ
- Zargin Tarayya Da Matar Aure: Miji Ya Ki Amincewa Da Hukuncin Kotun Da Ta Wanke Kwamishinan Jigawa
Za a mika kudirin kasafin kudin 2025 na naira tiriliyan 47.9 ga majalisar dokoki ta kasa domin tantancewa.
A cewar takardar da ofishin kasafin kudi na tarayya ya fitar, ana sa ran biyan basussuka, saboda yawan basussukan da ake bin kasar da kuma yadda babban bankin Nijeriya (CBN) ya kara kudin ruwa zuwa kashi 27.25.
Kudirin dokar ya zayyana yadda za a samu manyan kudaden shiga da manufofin kashewa a cikin 2025.
A karkashin kudaden shiga, gwamnatin tarayya na shirin samun naira tiriliyan 34.8 da naira tiriliyan 19.6 da naira tiriliyan 5.7 daga harajin man fetur da bangarori wadanda ba na man fetur ba, naira tiriliyan 2.87 daga kamfanonin mallakar gwamnati, naira tiriliyan 3.6 daga hanyoyin samun kudaden shiga masu zaman kansu da kuma naira tiriliyan 4.8 daga wasu hanyoyin.
Kudirin kashe kudi na gwamnati na shekara mai zuwa shi ne naira tiriliyan 47.9, wanda ya kunshi naira tiriliyan 14.2 na biyan bashi, naira tiriliyan 16.4 za a kashe wajen gudanar da manyan ayyuka, naira tiriliyan 15.38 na hidimar basussuka da kuma naira tiriliyan 2 na sauran abubuwan da za a yi.
Gwamnati ta amince da kalubalen tattara kudaden shiga, karancin mai da iskar gas, da hauhawar farashin tallafin man fetur a matsayin masu bayar da gudummawa ga gibin kasafin kudin tarayya.
Sai dai ana sa ran sauye-sauyen da aka yi a baya-bayan nan da suka hada da cire tallafin man fetur, da rage harajin da ake samu, da karuwar yawan danyen mai da ake hakowa za su rage matsin tattalin arziki.
Domin cike gibin kasafin kudin, gwamnati za ta ciyo bashi mai sassauci da kuma aiwatar da matakan tattara kudaden shiga.
Gwamnati na shirin kara zage damtse wajen inganta harkokin kudi ta hanyar karfafa tsarin kasafin kudi da kuma duba yadda ma’aikatu da hukumomi gwamnati suke kashe kudade.