Fadar Shugaban kasa ta kara zage damtse wajen rokon ‘yan Majalisar dokoki ta kasa da ta amince da kudurin gyaran fuska ga haraji.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa, shugabancin majalisar wakilai ya gayyaci shugabannin kwamitin majalisar domin yin wani muhimmin taro da nufin shawo kan ‘yan majalisar da su goyi bayan kudurin.
- An Sake Tallafa Wa Al’ummar Gambaru Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
- Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Tare Da Tarwatsa Ma’ajiyar Abincinsu A Tafkin Chadi
Majiyoyi sun yi nuni da cewa, fadar shugaban kasar na da burin ganin an amince da garambawul kan harajin kafin karshen shekara ta yadda kudurin zai fara aiki nan da ranar 1 ga watan Janairun 2025, tare da kasafin kudin 2025.
Wannan rokon ya biyo bayan matsin lamba daga gwamnonin arewacin kasar, wadanda ke kira ga ‘yan majalisar yankin da su bijirewa kudurin.
Kungiyar gwamnonin jihohin Arewa da masu rike da sarautun gargajiya daga yankin sun yi fatali da kudurin gyaran, wanda a cewarsu, za su cutar da yankin Arewa da sauran yankunan kasar.