Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah a wata tattaunawa ta tsaro da jami’an Isra’ila a daren Lahadi, in ji wata majiya mai tushe.
Majiyar ta ce, amma Isra’ila na da wata bukata ta musamman game da yarjejeniyar, wadanda ake sa ran mikawa gwamnatin Lebanon ranar Litinin.
- Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Sasanta Batun Nukiliyar Iran A Siyasance
- An Sake Tallafa Wa Al’ummar Gambaru Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
Ana ci gaba da tattaunawa kan bukatun da ake son cimmawa kafin tabbatar da amincewar yarjejeniyar.
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tana bukatar amincewar majalisar ministocin Isra’ila, wadda har yanzu ba ta yanke shawara ba.
A cikin ‘yan kwanakin nan, kungiyar Hizbullah ta yi nazari kan shawarar da Amurka ke goyon bayanta na tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 60 a yakin, wanda daga nan, ake fatan za ta iya zama tushen tsagaita bude wuta mai dorewa.