Da sanyin safiyar Litinin din nan ne kasar Sin ta yi nasarar harba sabbin taurarin dan adam guda biyu, ta amfani da rokar Long March-2C.
An harba taurarin samfurin Siwei Gaojing-2 03, da Siwei Gaojing-2 04 ne da karfe 8 saura mintuna 21 bisa agogon birnin Beijing, daga cibiyar harba kumbuna ta Jiuquan, dake arewa maso yammacin kasar, sun kuma shiga falakinsu cikin nasara.
Wannan ne karo na 547 da kasar Sin ta yi amfani da roka samfurin Long March wajen harba tauraron dan adam zuwa samaniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp