Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya ce Nijeriya na yin asarar sama da dala biliyan daya duk shekara sakamakon cutar zazzabin cizon sauro.
Pate, ya bayyanna hakan ne, yayin kaddamar da taron bayar da shawarwari da tuntuba kan yaki da cutar ta zazzabin cizon sauro a Nijeria, wanda aka yi a Abuja, a ranar Talata.
- An Fitar Da Tsarin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa A Fannin Raya Masana’Antu Da Rarraba Hajoji Na Beijing
- Yahaya Bello Ya Fada Komar EFCC, Zai Amsa TambayoyiÂ
A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labaran ma’aikatar, Alaba Balogun, ya fitar, ya ce Pate, ya ce zazzabin cizon sauro ba matsala ce ta rashin lafiya ba kadai, ta zama matsala ga tattalin arziki.
Ya ce, cutar na ci gaba da gagarumar illa a kan Nijeriya, inda ta ke da kashi 27 cikin dari na yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a duniya.
Ya ce kuma ce kashi 31 cikin darin na yawan mutanen da ke mutuwa a duniya a dalilinta .
Ministan ya kara da cewa Nijeriya ce ta fi fama da matsalar cutar, inda a 2022, sama da yara 180,000 ‘yan kasa da shekara biyar suka mutu a sanadin cutar.
”Wannan abu ne da za mu iya kaucewa.” In ji shi.
Ya bayyana yadda cutar ke kassara kasar ta bangarorin lafiya da kuma tattalin arziki.