Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta doke takwararta Real Madrid a wasan zagaye na biyar na gasar zakarun Turai ta bana a filin wasa na Anfield da ke birnin Liverpool.
Wasan ya matukar daukar hankalin masu sha’awar harkar kwallon kafa a duniya duba da cewa dukkanin kungiyoyin biyu babu kanwar lasa a wajen iya taka leda.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Tabbatar Da Samar Da Kayayyaki A Duniya
- Tattalin Arziki: Gwamna Lawal Ya Nemi Hadin Gwiwar Masu Zuba Jari Na Kasashen Afirka A Taron AFREXIM A KenyaÂ
Duk da cewa akwai da yawa daga cikin manyan ‘yan wasan Real Madrid da ke fama da rauni amma Liverpool ba ta samu damar huda ragar Galacticos din ba sai a minti na 52 inda Mac Allister ya jefa wa Liverpool kwallon farko.
Minti 24 tsakani Cody Gakpo ya jefa ta biyu wanda hakan ya sa Real Madrid ta koma matsayi na 24 a teburin gasar zakarun Turai ta bana.