Bayan fara fafutukar yaki da cin zarafin mata na tsawon kwana 16, shugabannin kasashen duniya sun nuna matukar damuwarsu dangane da karuwar annobar a Nijeriya.
Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya sun bayyana cewa, Nijeriya na bukatar kusan Naira tiriliyan daya; don magance cin zarafin da ake yi wa mata.
- Yadda Matatar Mai Ta Fatakwal Ta Fara Aiki
- Nijeriya Ta Shirya Magance Matsalar Almajirai – Tinubu Ga Macron
Sun kwatanta kudaden da ake kashewa wajen cin zarafin matan a Nijeriya da kimanin kashi 1.5 cikin 100 (N1.06 trillion) na tattalin arzikin da take samu a kowace shekara.
Shugabannin kasashen duniyar, sun bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da ma’aikatar harkokin mata ta 2024, da aka gudanar na tsawon kwana 16; domin fafutukar yaki da cin zarafin mata na wannan shekara a Abuja.
Da take gabatar da jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar Kula da Mata ta Majalisar Dinkin Duniya; Beatrice Eyom ta bayyana cewa, cin zarafin wani bangare na jinsi; wanda ya wuce batun musgunawa mata kadai ko wasu sauran jinsina, domin kuwa yana da tasiri wajen tauye ci gaba da kuma tattalin arzikin kasa.
“Idan muka duba, za mu fahimci cewa; kusan kashi 42 na matan Nijeriya ba masu kudi ba ne; idan muka kwatanta su da kashi 35 cikin 100 na maza, musamman idan kuma muka yi la’akari da matan da ke rike da mukamai a kasar kashi 5 ne kacal na wadanda aka zaba. Haka nan, Nijeriya ta fuskanci mummunar asara a bangaren tattalin arziki; wanda aka kiyasta cewa ya kai kimanin kashi 1.5 na kudaden da take samu a duk shekara, inda hakan ke kawo cikas ga ci gaban kasar.
“Wannan rikici na jinsi, ya wuce batun miji ya doki matarsa kadai. Abu ne wanda zai iya rage ci gaban tattalin arzikin kasa. Don haka, ba za ta taba rabuwa da talauci ba; muddun ba a rage ko kawo karshen cin zarafin da ake yi wa mata ba”, in ji Eyom.
Da yake kiyasta asarar da Nijeriya ta yi ta fuskar tattalin arziki (Kashi 1.5 cikin 100) da ke da alaka da cin zarafin mata, tiriliyoyin Nairori ne a kowace shekara, Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya; Mista Ndiamé Diop ya yi nuni da cewa, ba a yi la’akari da alkaluman da aka yi asara na sa’o’in aiki da kasuwancin da aka dakile jinsin matan ba.
“Tasirin cin zarafin matan ta fuskar tattalin arziki, na da matukar yawa. Kudaden da gwamnatin tarayya ke warewa don yaki da cin zarafin matan; ana karkatar da su ne wajen kula da lafiyar yara ko wasu nau’o’in kalubaben matsalar kiwon lafiya a kasar,” in ji Diop wanda wani jami’in Bankin Duniya ya wakilta a wurin taron.
Da yake mayar da martani game da koma bayan da ake samu a bangaren kudi, don magance matsalar cin zarafin ‘ya’ya mata da kuma kiran Eyom ga gwamnati da ta zuba hannun jari wajen aiwatar da manufofin jinsi, adalci da kuma hana cin zarafin mata, Diop ya ce; Bankin Duniya ya himmatu wajen ganin ya taimaka wa gwamnatin Nijeriya, domin yaki da wannan cin zarafi na mata.
“A cikin kudaden da suke ajiye a banki, kimanin dala biliyan 17; an ware dala biliyan 540, domin karfafa tattalin arzikin mata. A matsayinmu na banki, mun himmatu wajen tallafa wa Nijeriya tare kuma da inganta tattalin arzikin mata.
Har ila yau, mun mayar da hankali wajen kamfen din yaki da cin zarafin matan ta hanyar tanadar kimanin kusan dala biliyan 17, domin aiwatar da wannan kudiri”, in ji Diop.
Rahoton da LEADERSHIP ta bayar, bugu na 2024 na kamfen din shekara-shekara, mai taken ‘Towards Beijing +30: Hada kai don kawo karshen cin zarafi ga mata’, ya yi kira ga daidaikun mutane da kungiyoyin mata da kuma sauran kungiyoyi, da su yi kokarin daukar matakan kawar da cin zarafi ta hanyoyin da aka tsara kamfen din kowace rana.
A nata bangaren, Babbar Daraktar Cibiyar Sadarwa da Zamantakewar Al’umma; Madam Babafunke Fagbemi, ta bayyana matukar damuwarta; kan yadda ake ci gaba da samun karuwar cin zarafin matan a duniya.
Madam Fagbemi, a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ta ce; alkaluman baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar kan wannan lamari, ba kawai abin tayar da hankali ba ne; abu ne da ya kyautu a ce kowa ya farka daga barcin da yake yi tare da bayar da gudunmawa wajen kawo karshen wannan cin zarafi da ake yi wa wadannan mata da kuma sauran ‘yan mata.
Dangane da sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya, Ofishin Majalisar Dinkin Duniyar kan hana shan miyagun kwayoyi da aikata laifuka (UNODC) da aka yi wa lakabi da ‘Kisan da maza ke yi wa mata da ‘yan mata a 2023: Kididdigar da aka aiwatar a duniya ta tabbatar da cewa, a kullum ta Allah ana kashe mace ko budurwa a duk minti 10; ko dai miji ya kashe matar ko saurayi ya kashe budurwarsa ko kuma danginsu su yi kisan.
A 2023 kadai, mata da ‘yan mata kimanin 85,000 aka kashe da gangan a duniya, sannan kashi 60 cikin 100 na wadanda aka kashe din ma’ana kimanin su 51,000, sun mutu ne sanadiyyar mazajensu ko kuma dangin mazajen nasu.
Rahoton ya sake bayyana cewa, Afirka ce a gaba wajen samun yawan wadanda ke aikata wannan kisa a tsakanin ma’aurata da danginsu a 2023, sai kuma Kasar Amurka da sauran kasashe kamar irin su Australiya da sauran makamantansu. A Turai da Amurka kuma, yawancin matan da aka kashe a cikin gida; kashi 64 da kuma 58 cikin 100; mazajensu ne suka kashe su. Haka nan, a wasu yankunan kuma; dangin mazajen ne ke da hannu wajen aikata kisan.
Ko shakka babu, wadannan alkaluma sun nuna yadda ake cin zarafin mata da ‘yan mata, wanda kuma akwai bukatar hada hannu wuri guda; domin daukar tsauraran matakai.
Mai Dakin Tinubu Ta Nemi A Tallafa Wa Matan Da Abin Ya Shafa
Uwargidan Shugaban Kasar Nijeriya, Remi Tinubu; ta yi kira da a dauki matakin gaggawa na yaki da cin zarafin mata, a daidai lokacin da kasar ta shiga sahun kasashen duniya; domin tuna wa da ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya.
Wannan rana ta kasance ta farko cikin ranaku 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata, inda aka gudanar da wani gangamin wayar da kan al’umma tare kuma da yunkurin kawar da cin zarafin da ake yi wa mata da kuma ‘yan mata a duk shekara.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin da ta gabata, Uwargidan Shugaban Kasar; ta bayyana cin zarafin matan a matsayin guda cikin tauye hakkin Bil’adama da kusan za a iya cewa ya mamaye mata a duk inda suke a fadin duniya.
Ta kara da cewa, munanan ayyuka masu cutarwa a Nijeriya kamar batun auren wuri da kaciyar mata; na ci gaba da yaduwa, wanda galibi kuma ya samo asali ne daga al’adu ko kuma addinai.
“Koda-yake dai, muna samun ci gaba sosai; amma musamman a a yankunan karkara da wasu daga cikin marasa galihu; na ci gaba da kasancewa cikin wannan mummunan yanayi”, in ji ta.
Gwamnati Ta Kuduri Aniyar Kawo Karshen Lamarin– Shettima
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na inganta samar da daidaito a tsakanin jinsi ta hanyar sabbin manufofin gwamnatinsu.
Mataimakin Shugaban Kasar, ya kuma jaddada muhimmancin irin rawar da mata ke takawa; musamman wajen samar da daidaito a tsakanin al’umma.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Litinin; wajen taron murnar cika shekara 109 na uwargidan marigayi Cif Obafemi Awolowo.
Mataimakin Shugaban Kasar, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha ya fitar; ya yi kira da a sake sabunta kokarin kasa, don samar da dunkulalliyar al’umma, ta yadda mata za su samu dama wajen aiwatar da shugabanci; yana mai cewa, “Damar da kowace kasa ke bai wa mata, wata alama ce irin ta wayewar kasar.
Ya jinjina wa marigayiyar, inda ya bayyana ta a matsayin wata sarauniya ta daban da ke da kima da kuma kwarjini.
Sannan, ya kuma yaba da irin gudunmawar da ta bayar a Nijeriya tare da nuna goyon bayanta ga Maigidanta Cif Obafemi Awolowo tare kuma da fafutukar kare ‘yancin mata.
Za Mu Kawo Karshen Cin Zarafin Mata– Kakakin Majalisa
Shugaban Majalisar Wakilai ta Kasa, Hon. Abbas Tajudeen ya bayyana cewa; majalisar dokokin kasar za ta yi duk mai yiwuwa wajen kokarin kawo karshen cin zarafin mata da kuma ‘yan mata, nan ba da jimawa ba.
Abbas ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi a taron yaki da cin zarafin mata, wanda ya gudana daga harabar majalisar dokokin kasar zuwa hedikwatar ‘yansandan Nijeriya da ke Abuja; ranar Litinin da ta gabata.
Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar Majalisar Dokokin Kasar ne suka shirya taron, wanda ya yi nuni a kan nuna adawa da cin zarafin ‘ya’ya mata. Har ila yau, taron ya samu halartar kimanin mutum 1000; wadanda suka gudanar da tattaki don nuna goyon bayansu ga daukar kwararen matakai a Nijeriya.
Kakakin Majalisar Abbas ya sanar da cewa, majalisar dokokin kasar; za ta taka muhimmiyar rawar gani a shirin da ake kokarin aiwatarwa na yaki da cin zarafin mata; wanda ake sa ran aiwatar da shi nan ba da jimawa ba.
Ya ce, “Yau rana ce ta tahiri, wadda majalisar dokokin kasar ta zabi shiga wasu kungoyi na kasa; wadanda ke yaki da cin zarafin mata