Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya tura tawagar mu’amalar al’adu ta jihar Xinjiang ta kasar Sin, zuwa kasashen Turkiye, da Saudiyya da Qatar don gudanar da cudanyar al’adu.
Tawagar ta gudanar da rangadin daga ranar 20 zuwa yau Juma’a 29 ga wannan wata. Kuma yayin ziyarar, tawagar ta yi bayani a fannonin samun ci gaba mai inganci a sabon zamani, da yaki da ta’addanci, da kare hakkin dan Adam, da tabbatar da al’adun kabilu daban daban, da aiwatar da manufofin bin addinai cikin ‘yanci, da sa kaimi ga raya yanki mai muhimmanci, bisa shawarar zirin tattalin arziki na hanyar siliki da sauransu, don gwada nasarorin da aka samu yayin da ake aiwatar da manufar zamanintarwa iri ta kasar Sin a jihar Xinjiang.
- Ƙasurguman ‘Yan Bindiga 7 Sun Mika Wuya Ga Sojoji
- Kasar Sin Za Ta Yi Garambawul Da Bullo Da Sabon Ci Gaban Kasuwancin Fasahohin Zamani
Bangarorin kasashen uku sun amince da nasarorin da aka samu a jihar Xinjiang, a fannonin mai da hankali ga jama’a, da yin kwaskwarima mai zurfi a dukkan fannoni, da cimma burin samun ci gaba mai inganci, kana sun nuna kyakkyawan fata ga kara yin hadin gwiwa tsakaninsu da jihar Xinjiang a fannonin raya tattalin arziki da al’adu.
A nasa bangare, tsagin kasar Turkiye ya jinjinawa nasarorin da aka samu a jihar Xinjiang a fannonin bunkasa tattalin arziki, da hadin kan kabilu, da zaman jituwa a tsakanin addinai, da gadon al’adu da sauransu. Kana bangaren Saudiyya ya yabawa nasarorin da aka samu a jihar Xinjiang a aikin kawar da talauci. Yayin da shi kuma bangaren Qatar ya amince da nasarorin da aka samu a jihar Xinjiang, a fannin sha’anin kare hakkin dan Adam a jihar. (Zainab Zhang)