A gun taron albarkatun amfani da yanar gizo na kasar Sin karo na 5 da aka gudanar a yau Asabar, cibiyar sakwanni ta yanar gizo ta kasar Sin, ta gabatar da rahoton bunkasawa, da amfani da manhajar samar da nau’o’in bayanai ta fasahar AI na shekarar 2024, wanda ya yi nuni da cewa, ya zuwa watan Yuni na shekarar 2024, yawan masu amfani da manhajar samar da nau’o’in bayanai ta fasahar AI a kasar Sin ya kai miliyan 230.
Rahoton ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta kafa tsarin sana’ar fasahar AI a dukkan fannoni a mataki na farko, inda yawan kamfanonin da abin ya shafa ya zarce 4500, kana yawan kudin sana’ar ya kai kudin Sin Yuan kimanin biliyan 600.
Ya zuwa watan Yuli na shekarar 2024, yawan manhajojin samar da nau’o’in bayanai ta fasahar AI na kasar Sin da suka yi rajista, da samar da hidimomi ga jama’a ya kai fiye da 190, wadanda suke baiwa masu amfani da su bukatu a wannan fanni.
Sannu a hankali, kayayyaki masu amfani da fasahar AI suna shiga zaman rayuwar jama’a, wadanda kuma suke inganta zaman rayuwa da aikinsu baki daya. (Zainab Zhang)