Shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Faransa a ranar Litinin zuwa birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.
A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Onanuga, shugaban kasar zai jagoranci taro karo na 11 na hukumar hadin kan Nijeriya da Afirka ta Kudu (BNC) tare da shugaba Cyril Ramaphosa.
- Ana Ci Gaba Da Neman Wadanda Suka Bace Bayan Kifewar Jirgin Ruwa A Masar
- Dalilai 15 Na Muhimmancin Tsara Yadda Malami Zai Koyar Da Darussa A Aji (1)
“Taron wanda zai gudana a ranar Talata, 3 ga Disamba, zai kasance gabanin taron ministoci a ranar 2 ga Disamba, 2024, a ginin majalisar dokokin Afirka ta Kudu a Cape Town.
“Shugaba Tinubu da shugaba Ramaphosa za su tattaunawa a kan batutuwa da dama da suka shafi moriyar juna, a tsakanin harkokin kasashen biyu da na kasa da kasa.
“Taron na 11 na BNC zai gabatar da shawarwari a tsakanin fannoni guda takwas da suka hada da tuntuɓar juna kan siyasa, batun kaura, hada-hadar kuɗi, tsaro, masana’antu, zamantakewa, ma’adinai da makamashi, kasuwanci da saka hannun jari.”
A cikin sanarwar, Onanuga ya ce, jami’an kasashen biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna (MoU) da wasu yarjejeniyoyin.
A shekarar 1999 ne aka kafa hukumar hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu domin kara karfafa dankon zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.