Wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana matukar adawar kasar, da aniyar Amurka ta sayarwa yankin Taiwan na Sin din makamai, tare da gabatar da korafi ga gwamnatin ta Amurka kan haka.
Rahotanni na cewa, a jiya Asabar ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar da amincewa da sayarwa Taiwan makamai, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 385.
- Tinubu Zai Tafi Afirka Ta Kudu Daga Faransa
- Arsenal Da West Ham Sun Kafa Tarihi A Wasan Da Suka Tashi 5-2 A London
Game da hakan, kakakin na ma’aikatar wajen Sin ya ce wannan cinikayya halamtacciya ce, kasancewar ta sabawa ka’idar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyi 3 wadanda Sin da Amurka suka amincewa, musamman ma sanarwar bayan taro, ta ranar 17 ga watan Agustan shekarar 1982, kaza lika, matakin ya keta hurumin ikon mulkin kai na Sin da moriyar tsaron kasar.
A wani ci gaban kuma, wasu rahotannin na cewa jagoran yankin Taiwan Lai Ching-te, ya fara wani bulaguro da aka ce wai na “Yaukaka kawancen diflomasiyya” ne a yankin Fasifik, inda ya yada zango a jihar Hawaii ta Amurka.
Game da hakan, kakakin ma’aikatar wajen Sin ya ce kasarsa na matukar adawa da wannan mataki, kuma ba za ta amince da duk wani nau’i na hulda tsakanin Amurka da yankin Taiwan a hukumance ba. Har ila yau, ta yi Allah wadai da ziyarar da duk wasu shugabannin Taiwan za su gudanar a Amurka, karkashin ko wane suna ko manufa. Kana tana matukar adawa da duk wani hadin baki tare da Amurka, na tallafawa ‘yan aware masu rajin “Neman ‘yancin kan Taiwan”, da taimakawa ayyukan su. (Mai fassara: Saminu Alhassan)