Akalla jami’an ‘yansanda 4,449 ne suka kai karar rundunar ‘yansandan Nijeriya da babban sufetan ‘yansanda na kasa a gaban kotun da’an ma’aikata ta kasa da ke Abuja kan jinkirin aiwatar da karin girma.
Duk da karin girma da hukumar ‘yansandan ta amince da su kamar yadda doka ta tanada, jami’an na zargin cewa ba a yi musu ado da sabbin mukamai ba.
- AFCON: Magoya Bayan Napoli Sun Isa Cote de Voire Domin Mara Wa Osimhen Baya
- Ƴansanda Sun Kama Wani Matashi Kan Zargin Kashe Matar Aure
A ranar Talata ne aka dage ci gaba da sauraren shari’ar, wadda mai shari’a R.B. Haastrup ya jagoranta, inda za a ci gaba da shari’ar a ranar 18 ga watan Disamba.
Lauyan wadanda suka shigar da kara, Muka’ila Mabo, ya bukaci kotun da ta bayar da umarnin tilasta wa rundunar ‘yansandan Nijeriya da babban sufeta na kasa aiwatar da yanke hukunci a cikin sashi na 19 na dokar rundunar ‘yansandan Nijeriya, wanda ya amince da karin girma ga jami’an 4,449.
Mabo ya bayar da hujjar cewa hukuncin ya yi daidai da sashe na 6 (1) (a) na dokar rundunar ‘yansandar Nijeriya da sashe na 16 (3) (a) na dokar ‘yansanda.
Da yake magana kan lamarin, Mabo ya ce, “Ya kasance al’ada ce tsakanin rundunar ‘yansandan Nijeriya da hukumar kula da yarkokin ‘yansanda, wadda ta samu amincewar shari’a daga kotun koli, ita ce ke da alhakkin nadawa da karin girma da kuma da’a ga dukkan jami’an ‘yansanda ban da babban sufetan ‘yansanda na kasa.”
A halin da ake ciki, lauyan da ke wakiltar rundunar ‘yansandan Nijeriya, ACP Isa Garba, ya ki bayar da cikakken bayani, inda ya bayyana cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar zai fi dacewa wajen tuntubar al’amarin.