Yau Litinin, ofishin tsara babbar liyafar taya murnar bikin sabuwar shekarar Sin bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin ta 2025 na babban rukunin gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG ya gabatar da alamar bayyana kyakkyawar fata ta sabuwar shekara da ake kira “Si Shengsheng”, don yi wa Sinawa a duk fadin duniya fatan alheri a cikin sabuwar shekara mai tafe.
An tsara wannan alama mai siffar maciji bisa al’adun gargajiyar Sinawa, wadda ke da kyau da kuma ma’anar gargajiya.
Ana kusantar wannan gagarumar liyafa duba da bayyanar alamar “Si Shengsheng” ga jama’a, wadda ke gayyatar kowa da ya kalli bidiyon wannan liyafar, tare da maraba da sabuwar shekarar gargajiyar Sin ta maciji mai cike da farin ciki da alheri. (Amina Xu)