Rundunar sojin Nijeriya, sun yi nasarar hallaka dimbin ‘yan bindiga a kauyen Galadima da ke karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara.
A cewar sanarwar da jami’in da ke kula cibiyar yada labaran rundunar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya fitar, hakan ta faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace Wasu A Sakkwato
- Alternative Bank Shi Ne Mafi Inganci Da Baya Amfani Da Kuɗin Ruwa Da Zuwa Da Fasaha A 2024
“Nan da nan dakarun suka mayar da martani ta hanyar kai dauki tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
“Yayin sintirin, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’adda da suka yi musu kwanton bauna a wurare biyu.”
“Dakarun sun yi nasarar tarwatsa wuraren kwanton baunan tare da hallaka wasu ‘yan ta’addar sannan wasu suka tsere.”
Ya kara da cewar aikin wanzar da zaman lafiyar na da nufin kawar da duk wata barazanar ‘yan ta’adda a shiyyar Arewa Maso Yammacin Nijeriya.