Sin babbar kasa mai tasowa, mai karfin tattalin arziki na biyu a duniya, kuma babbar abokiyar huldar kasashen Afrika, na ci gaba da nunawa duniya cewa, ita din mai neman ci gaban duniya ce, haka kuma kawa ce abin dogora a ko da yaushe.
Ba abun mamaki ba ne yadda na fara da yabon kasar Sin, saboda har kullum kasar na ci gaba da kasancewa a bar yabo da koyi.
- Shawarar BRI Na Samar Da Wani Yanayi Mai Yakini Ga Tattalin Arzikin Duniya
- Alternative Bank Shi Ne Mafi Inganci Da Baya Amfani Da Kuɗin Ruwa Da Zuwa Da Fasaha A 2024
A ranar Lahadin da ta gabata, kasar ta kaddamar da manufar dauke haraji na kaso 100 bisa 100 kan wasu hajojin dake shiga kasar daga kasashen Afrika masu karancin wadata dake da huldar diplomasiyya da ita.
Shin daga cikin kasashe masu kiran kansu manya ko ke shafawa kasar Sin bakin fenti a wajen kasashen Afrika, suna cewa tana kokarin dana musu tarkon bashi da sauran karairayi, akwai wadda ta yi wa kasashen Afrika irin wannan tagomashi? Kasar Sin ce babbar kasa mai tasowa ta farko, kuma ta farko cikin kasashe masu karfin tattalin arziki da ta dauki irin wannan mataki.
Hakan da ta yi, ya sake bayyanawa duniya kyakkyawar niyyar kasar Sin ta ganin kasashe masu karancin kudin shiga sun samu damar fitar da kayayyakinsu zuwa kasarta domin cin gajiyar babbar kasuwarta tare da samun wadata da ci gaba. Har ila yau, ta sake tabbatar da manufarta ta sake fadada bude kofa ga kasashen waje domin su ci gajiyar gogewarta da ci gabanta.
Kamar yadda na saba fada, ci gaban kasar Sin ci gaba ne ga sauran kasashe ba kalubale ba. Kuma kasar ba ta kyashin ci gaban sauran kasashe, sabanin yadda wasu ke yi mata bita da kulli da kokarin ganin ta durkushe. Yayin da take samun ci gaba ta hanyar kirkire-kirkiren fasahohi da aiwatar da sabbin dabaru, kasashe masu son ci gaba da kaunar zaman lafiya, na iya hada gwiwa da ita domin raya kansu. Don haka duk mai son ganin durkushewar kasar Sin, to ba da ci gabanta kadai yake adawa ba, har da na kasashe masu tasowa da ma sauran kasashen duniya ba ki daya. (Fa’iza Muhammad Mustapha)