• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudurinsa Na Bai Wa Ɓangaren Shari’a ‘Yanci Don Samar Da Adalci A Zamfara

by Sulaiman
11 months ago
Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta duƙufa wajen ba da fifiko ga tsare-tsare da ke inganta tabbatar da adalci a kan lokaci da kuma kare ’yancin ɓangaren shari’a.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron ƙara wa juna sani ga alƙalai da ma’aikatan kotuna a babbar kotun shari’a ta Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a harabar babbar kotun da ke Gusau.

  • Babbar Kasa Mai Farar Aniya: Shin Har Yanzu Akwai Masu Son Lalata Dangantakar Sin Da Afrika?
  • Nakasa A Mahangar Karin Magana: Guzurin Ranar Nakasassu Ta Duniya

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, taron ya samar da wata dama ga jami’an shari’a da masu ruwa da tsaki domin tantance ayyukan da bangaren shari’a ke yi, da gano ƙalubale, da kuma kafa sabbin manufofi.

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

A jawabinsa na bufe taron, Gwamna Lawal ya amince da jajircewa da jagoranci na ƙwarai na Babbar Alƙalin Alƙalan Jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu, OFR, FNJI, da ɗaukacin bangaren shari’a bisa jajircewarsu na sauke nauyin da aka ɗora musu.

Ya ce, “jajircewarta wajen tabbatar da adalci yana ƙara ƙwarin gwiwa da kuma ƙara wa bangaren shari’a aminci a matsayin wata cibiya mai muhimmanci a tsarin dimokuraɗiyya. Wannan gwamnati ta tsayu tsayin daka wajen tallafa wa bangaren shari’a a dukkan ayyukanta.

“Gwamnatina za ta ci gaba da ba da fifiko ga shirye-shiryen da za su inganta samar da adalci a kan lokaci da kuma kare ‘yancin wannan bangare na gwamnati.”

Gwamna Lawal ya bayyana cewa, taron ƙara wa juna sanin na da matuƙar muhimmanci. “Zai inganta fasaha da kuma ilimantar da mahalarta domin su kasance cikin shiri sosai don yin hidima da biyan buƙatun jama’a. Jama’ar mu na kallon ku a matsayin matita ga talakan ƙasa wajen ganin ya samu adalci tare da kare haƙƙinsa. Dole ne jami’an shari’a da ma’aikatan su kasance cikin shiri sosai don cimma waɗannan manufofi, musamman a waɗannan lokutan da ake fuskantar ƙalubale.

“Babbar Alƙalin Alƙalai, alƙalan babbar kotun jihar Zamfara, manyan mahalarta taron, abin farin ciki ne ganin irin matakan da hukumar shari’a ke ɗauka wajen tsare-tsaren ma’aikatan Majistare da sauran ma’aikatan shari’q domin tabbatar da adalci.

Gwamnan ya kuma buƙaci bangaren shari’a da su yi taka-tsan-tsan a kan wasu ’yan tsirarun da ɗabi’unsu za su iya gurgunta mutuncin wannan hukuma. “Ganowa tare da magance rashin ɗa’a a bangaren wani nauyi ne da ke buƙatar himma, mutunci, da sadaukarwa.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya
Manyan Labarai

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa
Manyan Labarai

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025
Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
Labarai

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
Next Post
Sin Ta Yi Maraba Da Amincewar Da UNGA Ya Yi Da Kudurin Wanzar Da Zaman Lafiya Da Kasar Ta Gabatar

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
tinubu

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.