Annabi (SAW) ya tambayi Jabiru bin Abdullahi kan Matar da ya aura, ya ce masa, Budurwa ka aura ko Bazawara, sai ya ce, Bazawara, Annabi (SAW) ya ce masa kana yaro za ka auri Bazawara? Sai Jabiru ya ce, ya rasulallahi, mahaifina ya rasu ya bar min kannai mata, budurwa ba za ta iya zama da su ba, shi yasa na auri Bazawara.
Ta shida, akwai Duba’atu bintu Amirin, Annabi (SAW) ya nemi aurenta a wurin Danta, shi ne Salamata bin Hashim, sai dan ya ce, ya rasulallahi bari in nemi shawararta, wata kila a wurin cikin sahabbai wasu suka ce ya rasulallahi, ta tsufa, yayin da yaron ya dawo, ya ce ya rasulallahi, ta ce ta yarda, sai Annabi (SAW) ya yi shiru bai ba shi amsa ba. Annabi (SAW) bai aure ta ba.
Ta Bakwai, akwai ‘yar Sayyidina Hamza, baffan Annabi (SAW), ita kuma dangi ne suka nemi Annabi (SAW) ya aure ta, sai ya gaya musu cewa, Sayyada Halima ta shayar da Mahaifinta (Sayyadina Hamza) kamar yadda ta shayar da ni (Annabi (SAW)) don haka, ‘yar Sayyadina Hamza ‘ya take a wurina. Haramun ne aure a tsakaninmu.
Ta takwas, akwai Azzatu bintu Abi Sufyanu, ‘yar uwarta (Matar Annabi (SAW), Ummu Habiba) ita ta ce ya rasulallahi ka nemi ‘yar uwata, sai ya ce mata, ba ta halatta a gare ni ba sabida ina aurenki (Ummu Habiba).
Haramun ne a hada ‘yan uwa biyu a wuri daya, sai dai a saki daya, ko kuma in ta rasu, da fadin Ubangiji cewa: “wa’an tajma’u bainal uktaini illa ma kad salaf: Allah ya haramra muku hada ‘yan uwa mata a gidan aure daya”
Kila an ce, Annabi (SAW) ya nemi wata Mata ‘yar Kabilar Jundu’a amma bai tare da ita ba, amma wasu masu ruwaya sun yi inkarin wannan ruwayar.
Amma Malamai sun ruwaito cewa, Annabi (SAW) yana da Kuyangi Hudu: Ta farko, Mariyatul Kibdiyya – ita ta haifi Sayyadina Ibrahimal Mu’azzam, ‘yar Misra ce, Mukaukisu Sarkin Misra, shi ya bai wa Annabi Ita da ‘yar uwarta, Sirina, Sai Annabi (SAW) ya dauki Mariyatu, ita kuma Sirina ya bai wa Sahabinsa, Mawakinsa Hassanu Bin Sabitu. Sayyada Mariyatu, ta rasu cikin Kalifancin Sayyadina Umar, an bizne ta a makabartar Baki’a.
Ta biyu, akwai Raihanatul Kuraiziyyatu, Bayahudiya ce ‘yar bani Kuraizah, ta rasu kafin rasuwar Annabi (SAW).
Ta Uku, Matar Annabi (SAW), Zainabu bintu Jahshin ce ta bai wa Annabi (SAW) baiwarta, kamar yadda Matar Annabi Ibrahim Saratu ta bai wa mijinta baiwarta, Hajaru.
Ta hudun, Annabi (SAW) ya same ta ne a cikin ganimar Yaki ta zo a rabonsa, sai Annabi (SAW) ya yi sa-daka da ita.
Salma, baiwar Sayyada Safiyya matar Annabi ce ko kuma baiwar Annabi (SAW), an ruwaito ta ce, wata rana Annabi (SAW) ya kewaya matansa su tara (a Lokacin) duka a dare daya, sai dai bayan kwanciya da duk daya sai ya yi wanka. Annabi (SAW) ya ce yin wanka kafin zuwa ga wata bayan wata, shi yafi tsafta da lafiya.
Annabi Sulaiman (AS) ya fada yana cewa, na yi rantsuwa sai na kewaya Matana 100 a cikin daren nan, an ruwaito cewa Matayensa sun fi 100 ko kuma 99. Bayan ya yi rantsuwa a kan kewaya 100 a dare daya, Allah ya cika masa rantsuwarsa na bashi ikon kewayawa.
Yadda yazo a ruwaya, “wata rana Annabi Sulaiman, yana shirin fita yaki fi sabilillah, sai ya yi rantsuwa cewa, zai kewaya Matansa 100, kuma kowacce sai ta samu juna-biyu ta haifar masa Da Namiji Sadauki wanda za yi yaki fi sabilillahi, sai ya yi mantuwa bai ce ‘insha Allah’ ba. A cikin 100, ba wacce ta dauki Juna-biyu sai daya tak, ita ma ta haifi rabi.” Malamai sun ce wannan ayar tana magana ne da Annabi Sulaiman: “wa’alkaina ala kursiyyihi jasadan summa anab”.
Bayan haihuwar rabin dan jariri, Annabi Sulaiman ya kai kara wurin Ubangiji yana magiya da cewa, ya Ubangiji na kewaya Matana 100 da nufin su haifar min ‘ya’ya da za su yi yaki fi sabilillah amma daya ce ta haihu, shima rabi, sai aka yi masa wahayi cewa ya manta bai ce “insha Allah” ba. Amma wannan rabin in kana so ya cika ya rayu ga yadda za ka yi: Ka kira wazirinka da Matarka da Kanka, kowa ya fadi wani sirrin shi wanda babu wanda ya sani kuma bai so kowa ya sani. Sai Waziri ya ce sarki ya fara, bayan takaddama tsakanin su Ukun, sai Waziri ya yarda ya fara.
Waziri ya ce: Sarki ina neman tuba, duk da cewa kai sarkina ne, da yawan lokuta kake turowa a kira ni, nake fada a zuciya cewa ‘Ni sarki ya dame ni da kira’, sai daya cikin Ukun jikin jaririn ya tofo.
Mata, Uwar jariri ta ce: ina neman yafiyar sarki, duk da cewa Mijina Annabin Allah ne kuma Sarki amma na fi son a ce Saurayi ne ya aure ni ba tsoho ba. Sai kashi biyu cikin Ukun jikin jaririn ya tofo.
Sarki, Annabi Sulaiman ya ce: Duk da ni Annabin Allah ne, ya yi min Ni’imah kala-kala, ya gudanar min da Ruwan tagullah ina kere-kere da ita amma da yawa in mutane suka zo min, ina cewa, ina ma masu ba ni ne ba masu karba ba. Daga nan sai yaro ya cika gaba daya.
Kamar yadda muka fada a farkon karatu, muna magana kan abubuwan da ake son mutum ya yawaita, ga Annabi Sulaiman an ruwaito ya kewaya mata 100 cikin dare daya, me cewa, an ci mutumcin Annbi (SAW) sabida an ce ya kewaya mata tara a dare daya, yawan mata, yana daga cikin alfaharin maza a al’adar halittarsu, Annabi (SAW) ya fi kowa a kan komai.
Abdullahi bin Abbas, ya ruwaito cewa, Annabi Sulaiman (AS), Allah ya bashi Ruwan maniyyin Namiji 100, yana da Mata 300, sa-daka 300.
Malam Nakkashi ya ruwaito cewa, Annabi Sulaiman (AS) yana da Mata 700 da sa-daka 300, Annabi Dauda (Mahaifin Annabi Sulaiman) a bisa tsantseninsa, ya kasance bai cin komai sai daga Sana’arsa, yana da Mata 99 sai ya cika ta 100 din da Matar kwamandan yakinsa, bayan rasuwarsa, sai Annabi Dauda ya aure ta (ita ce mahaifiyar Annabi Sulaiman).
Yadda tarihin yake, Babban kwamandan yakin Annabi Dauda yana da Mata kyakkyawa, wata rana sai Annabi Dauda ya ganta sai Allah ya yi masa kashafi cewa, wannan Matar ita ce za ta Haifa masa Annabi Sulaiman. Nan da nan, Annabi Dauda ya dinga shirya yakoki sabida wannan kwamanda ya rasu shi kuma ya auri Matarsa, hakan kuma aka yi a wani yaki, kwamandan ya rasu.
Annabi Dauda yana da Mata 99, kwamanda daya tak amma Annabi Dawud ya ganta yana son ta. A Zahiri sabo ya yi kamar irin abin da ya faru da Annabi Adam (AS), ya ci bishiyar da aka hana shi amma kuma cin bishiyar ya samar da Annabawa da Waliyyai. Auren Annabi Dawuda da Matar kwamanda ya samar da Annabi Sulaiman da ya mulki Duniya.
Allah tabaraka wata’ala ya tabbatar da hakan da fadinsa: ”inna haza, akhi lahu tis’un wa tis’una na’ajatan waliya na’ajatun wahidah, fakala akfilniha wa’azzani fil kidab, kala lakad zalamaka bi su’ali na’ajatika ila ni’ajihi, wa inna kasiran minal kulada’i layabgi ba’aduhum ala ba’adin illallazina amanu wa’amilus salihatt, wa kalilum mahum, wazanna Dawudu annama fatannahu fastagfara rabbahu wa karra ra’ki’an wa’anab, fagafarna lahu zalik, wa’inna lahu indana lazulfa wa husna ma’ab”
Wata rana, Annabi Dawud, yana cikin dakinsa yana Ibada, sai ga Mutane biyu sun shigo ba tare da masu gadinsa sun sani ba, sai ya razana, ya ce musu ku kuma su waye kuma daga ina, sai daya ya ce “wannan dan’uwana ne, yana da shanu 99, ni kuma ina da daya, amma ya matsa min sai na ba shi ita, dole na ba shi ita sabida ya rinjaye ni a zance ”, bayan Annabi Dawudu ya yi musu hukunci ya tabbatar da cewa mai 99 ya zalumci mai daya sai suka koma.
Nan take, Annabi Dawuda ya fahimci cewa, ya yi wa kansa hukunci ne, sai ya nemi tuba kuma Allah ya gafarta masa.