Tafiyartar da harkokin banki a duniya na iya sa mutum ya jin kamar ya yi kokarin nemo hanyar da ta dace duk inda take, musamman ga wadanda suka dade suna jin dadinsa a shekaru da dama.
Sanin hakan, Bankin Stanbic IBTC ya samar da babban asusun ajiya na ‘yan kasa, wani tsari na sauyi salo wanda zai sa harkar banki ta samu sauki da kuma amfanar mutane masu shekaru 50 zuwa sama, wadanda aka kiyasta kusan miliyan 15 na al’ummar Nijeriya sama da miliyan 200.
- Ƴansanda Sun Hana Sarki Sanusi II Tafiya Bikin Naɗin Sabon Hakimin Bichi
- Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Waɗanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara
Babban asusun ajiya na ‘yan kasa ba kawai wani samfurin banki ba ne. Shaida ce ta sadaukarwar Stanbic IBTC don biyan bukatu musamman na yawan mutanen da suka tsufa. Wannan lamarin dai ya hada da komai daga adana dukiya da shawarwarin harkokin kudade zuwa dandamali na banki mai amfani da hanyoyin sadarwar da tabbatar da cewa manyan ‘yan kasa suna da duk abin da suke bukata don jin dadin da samun lafiya a lokacin da aka yi ritaya.
Bankin Stanbic IBTC ya fahimci cewa bukatun banki suna tasowa, yayin da abokan ciniki ke tafiya cikin matakai daban-daban na rayuwa. Babban asusun ajiya na ‘yan kasa shi ne mafita na banki ga mutane masu shekaru 50 zuwa sama, kamar yadda ake nutsewa cikin harkokin kasuwanci da ke cike wani gibi a cikin ayyukan banki wanda ya dace da bukatun kudi na musamman ga al’ummar da suka yi ritaya. Ba wai kawai game da tanadi don yin ritaya ba ne, har da yadda rayuwa za ta yi dadi tare tsare kudade cikin sauki. Wannan shi ne inda babban asusun ajiya ya shigo, yana ba da cikakkiyar ayyuka da aka tsara ga mutane wadanda suka tsofa.
A jigon dabarun samar da babban asusun ajiya ya ta’allaka ne ga kokarin adana kudade. Duk da haka, wannan ya kasance wani mafari ne. Sanin muhimmancin saukin yin amfani da magance abubuwa yana habaka abokantakar mai amfani. Tabbatar da sanin ilimi, yana ba da damar samun zaman lafiya na kudi, yana karfafa mutane su kasance da masaniya da sarrafa kudinsu yadda ya kamata.
Ko abokan ciniki suna neman hanyar tsare kudadensu, kariyar kadara ta hanyar zabubbukan inshora iri-iri, ko ingantattun hanyoyin sadarwar don matsalolin kiwon lafiya, babban asusun ajiyar ‘yan kasa ya kasance yana biyan wadannan bukatun.
Bude babban asusun ajiya ta na Bankin Stanbic IBTC ya zarce sarrafa harkokin kudi kawai, yana sauya rayuwar wadanda suka yi ritaya. Yana shelanta sabon zamani a harkar banki ga mutanen da suka kai shekaru 50 zuwa sama, yana habaka kwarewar banki. Yana gabatar da mafita na harkokin banki, ya kasance hadin gwiwa ne tsakanin Bankin Stanbic IBTC da abokan cinikinsa masu kima don sadar da amintaccen kwarewa a cikin harkokin banki.