Wani abu ya sake tashi a yankin Dansadau na karamar hukumar Maru da ke Jihar Zamfara, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’ar yankin kan matsalar tsaro.
A ranar Juma’a, bama-bamai biyu sun tashi a kan hanyoyin Dansadau-Malamawa da Malele.
Daya daga cikinsu ya lalata wata mota mai dauke da kayan abinci da ke kan hanyarta na zuwa kasuwar mako-mako ta Dansadau, amma babu wanda ya ji rauni.
Wannan shi ne karo na uku da bam ke tashi a yankin cikin mako É—aya.
A ranar Laraba, bam ya hallaka mutane 12 bayan ya rushe wata gada a kauyen Yar Tasha, inda ya samu wata mota mai É—auke da fasinjoji.
A ranar Lahadi kuma, wata motar kirar bas mai É—aukar mutum 18 ta taka bam, inda direban motsr ya rasa ransa nan take.
Rundunar ‘yansandan jihar, ta alakanta hare-haren da wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda mai suna Lakurawa.
Ana zargin kungiyar da dasa bama-bamai a kan manyan hanyoyi don kai wa matafiya hari.
Jama’a sun bukaci hukumomin tsaro su gaggauta daukar mataki don tabbatar da zaman lafiya.