An saka jimillar magungunan cututtuka 13 da ba kasafai ake kamuwa da su ba cikin jerin tsarin inshorar magunguna na kasar Sin na baya-bayan nan, wanda ya kawo adadin irin wadannan magungunan da ke cikin tsarin inshorar kasar zuwa sama da 90.
Saboda karancin wadannan cututtuka, da karancin adadin masu kanuwa da su, da yawan kudin bincike da habakawa, wadannan cututtukan da ba kasafai ake samun su ba sun kasance fannonin da ba a mai da hankali sosai a fagen kiwon lafiya. Kaza lika, ta hanyar kokarin da hukumomi ke yi, kasar Sin ta gaggauta gina hanyar yin rigakafi da magance irin wadannan cututtuka, tare da samar da karin magunguna masu sauki ga marasa lafiya.
Baya ga samar da karin magunguna, kasar Sin ta kuma inganta hanyar hadin gwiwar kasa da kasa don gano cutattukan da ba kasafai ake kamuwa da su ba da magance su. Ya zuwa Oktoban 2024, fiye da cibiyoyin kiwon lafiya 400 ne suka shiga cikin wannan tsarin, wanda ke kunshe da hanyoyin tuntubar likita da tsarin ba da jinya ta yanar gizo wanda ya hada dukkan yankunan larduna a duk fadin kasar. (Mohammed Yahaya)