Sanatocin yankin Kudu Maso Gabas, sun roki a sake nazarin kudirin haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisa.
Shugaban sanatocin yankin, Sanata Enyinnaya Abaribe, wanda ke wakiltar Abia ta Kudu a jam’iyyar APGA, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron sanatocin jihohin yankin guda biyar.
- ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
- Kwamitin Kolin JKS Ya Gudanar Da Taron Tattaunawa Don Neman Shawarwari Kan Aikin Tattalin Arziki
Sanata Abaribe ya ce ba wai suna son a yi watsi da kudirin harajin ba ne, sai dai suna so a yi karin tattaunawa da samun lokaci don tuntubar wadanda suke wakilta da sauran masu ruwa da tsaki.
“Mun yi nazari sosai kan kudirin harajin, kuma mun ga akwai bukatar mu tattauna tare da mutane daga yankinmu.
“Wannan zai tabbatar da cewa duk wata doka da aka kafa za ta amfani al’ummar Nijeriya, musamman yankinmu,” in ji Abaribe.
Sanatocin sun yi kira da a ba su damar yin aiki tare da wakilansu domin ganin an cimma matsaya mai amfani ga kowa da kowa.