Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya bayar da fifiko kan samar da abinci ga ‘yan kasa, domin yana son ganin babu wanda zai kwana da yunwa.
Karamin ministan noma, Aliyu Abdullahi, ya ce tun bayan hawan shugaba Tinubu a watan Mayun 2023, gwamnati ta kaddamar da shirye-shiryen tabbatar da wadatar abinci a kasar nan.
- ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
- Jami’ar Kwara Ta Rage Wa Masu Bukata Ta Musamman Kudin Karatu
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Sunrise Daily, ministan ya ce shugaba Tinubu ya mayar da hankali sosai kan noma domin samar da abinci da kuma bunkasa tattalin arziki.
A cewarsa, shugaba Tinubu ya damu da matsalar karancin abinci, kuma kullum yana fatan Nijeriya ta zama kasar da babu wanda zai kwana da yunwa.
Hauhawar farashin kayan abinci a baya-bayan nan ta jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a kasar nan.
Hakan ne ya sa gwamnatin tarayya ta fito da wasu matakai na tallafi, ciki har da rabon abinci don rage radadin wahala ga miliyoyin ‘yan Nijeriya.