Cikin taron manema labaran da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira a yau Alhamis, jami’in ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an cika shekaru 10 da kaddamar da aikin farko na layin gabas da na tsakiya na shirin janyo ruwan dake kudancin kasar Sin zuwa arewacinta.
Har ila yau, cikin wadannan shekaru 10, an riga an yi nasarar janyo ruwan fiye da kyubik mita biliyan 76 da miliyan 700 daga kudancin Sin zuwa arewacinta.
Jami’in ya kuma kara da cewa, ana kara ba da tabbacin samar da ruwa ga al’ummomi da masana’antun dake zaune a wuraren kusa da aikin, sakamakon ci gaba da habaka yankunan samar da ruwa masu nasaba da aikin, da gudanar da harkar da ta tallafa wa al’ummomi miliyan 185 dake zama cikin manya da matsakaitan birane guda 45. A sa’i daya kuma, ingancin amfanin ruwa a wuraren ya kasance kan gaba a duk fadin kasar Sin, sakamakon matakan tsimin ruwan da aka dauka. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp