Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya sallami Dr. Abdullahi Baffa Bichi, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), da ƙarin kwamishinoni biyar daga muƙamansu a wani tankaɗe da rairaya a gwamantinsa da aka sanar a yammacin yau Alhamis.
Hakanan, Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin jihar Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya samu sauyi inda aka soke ofishinsa daga aiki gaba ɗaya.
A cikin sanarwar da kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar, an lissafa kwamishinonin da aka sallama, wanda suka haɗa da Ibrahim Jibril Fagge (Kuɗi), Ladidi Ibrahim Garko (Al’adu da yawon buɗe ido), Baba Halilu Dantiye (Bayanai da Harkokin Cikin Gida), Shehu Aliyu Yammedi (Ayyuka na musamman), da Abbas Sani Abbas (Ci gaban ƙasa da al’ummomi).
- Dubban Mutane Sun Halarci Taron Mata Network A Kano
- Ma’aikacin Asibiti Ya Dawo Da Naira Miliyan 40 Da Aka Manta A Kano
Dawakin-Tofa ya bayyana cewa wannan canjin yana daga cikin ƙoƙarin inganta aikin gudanarwa da sabunta tsarin siyasa. Sia dai kuma, an bayyana cewa Dr. Bichi an sauke shi ne daga muƙaminsa ne saboda dalilan lafiya.
Amma duk da haka ana ganin kamar akwai wani dalilin saɓanin wanda aka bayyana. Wasu na ganin akwai yunƙurin yin sabon zubi na matasa masu jini a jika musamman waɗanda tsarin kwankwasiyya ya tura karatu.
Wannan hasashen zai gasgata ne ko akasinsa bayan an fito da sunayen waɗanda zasu maye gurbinsu.