Gwamnatin tarayya na shirin fara rabon mitan wutar lantarki guda miliyan 10 a farkon kwatan shekarar 2025, a karkashin shirin shugaban kasa na samar wa ‘yan Nijeriya mitar wutar lantarki.
Ta hanyar wannan shirin, gwamnatin tarayya na da burin cike gibin da ke akwai tare da kawo karshen biyan kudin wuta ba bisa ka’ida ba a Nijeriya, ta hanyar samar da mitoci miliyan biyu a duk shekara na tsawon shekaru biyar masu zuwa, daga farkon rubu’in shakarar, kamar yadda mai ba da shawara na musamman ga ministan wutar lantarki, Tunji Bolaji, ya shaida wa manema labarai.
- Tashar Wutar Kainji Da Jebba Sun Yi Asarar Naira Biliyan 30 Sakamakon Katsewar Wutar Lantarki
- Kasar Sin Ta Daukaka Kara Zuwa WTO Game Da Hukuncin Karshe Kan Matakin EU Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin
Wannan shiri wanda ya samu goyon bayan kasafin kudi na naira biliyan 700 tare da hadin gwiwar masana’antun cikin gida don samar da mitoci, na da nufin magance gagarumin gibin da ke tattare da mitoci, inda kusan mutum miliyan 5.99 ne kawai daga cikin miliyan 13.19 da suka yi rajista a yanzu.
Bayanai da ake samu sun nuna cewa ya zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2024, mutum 5,993,340 (kashi 45.43) ne kawai daga cikin 13,192,573 da suka yi rajistar masu amfani da wutar lantarki.
Idan ba a manta ba a watan Oktoba ne ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta sayi mitoci miliyan 1.3 a karkashin shirin DISREP, inda ya ce Nijeriya za ta samu mitoci miliyan 1.3 tsakanin watan Disamba 2024 zuwa kashi na biyu na shekarar 2025.