An tabka asara a tashoshin samar da wutar lantarki na Kainji da Jebba, biyo bayan katsewar baban layin samar da wutar lantarki, inda asarar ta kai ta Naira biliyan 30.
Wannan asarar dai, ta auku ne, a tsakanin shekarar 2022 and 2024.
- Netanyahu Ya Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Da Hizbullah
- Tarihi Zai Yi Tir Da Matakin Amurka Na Hawa Kujerar Na Ki Game Da Burin Tsagaita Wuta A Gaza
Idan za a iya tunawa, katsewar babban layin wutar lantarkin na kasa na baya bayan nan, ya katse ne a ranar Alhamis da ta gabata, wanda hakan ya nuna cewar, ya katse sau sha daya a 2024.
Matsalar dai, ta janyo dakatar da gudanar hada-hadar kasuwanci da kuma jefa gidajen kasar da dama, a cikin yanayi na duhu.
Masu amfani da wutar, kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) da sauran masu ruwa da tsaki, duk son koka a kan katsewar, ta shafi harkokin kasuwanci.
Kazalika, Gwamnatin Tarayya, ta dora laifin yawan samun lalacewar babban layin samar da wutar a kan lalata na’urorin samar da wutar da kasancewar ana samar da wutar da kayan da tuni, suka tsufa.
Bugu da kari, Gwamnatin ta ce, ba a kuma yawan gyra na’urorin da kuma zargin yin zagon kasa na wasu mahara da kai wa layin samar da wutar hari .
Wani kundin bayanai da aka samu a ranar Alhamis da ta wuce ya nuna cewa, an samu asara a manayn tashoshin biyun na samar da wutar, da ta kai ta Naira biliyan 30.55, wanda wannan asarar ita ce mafi muni da aka samu a wannan shekarar.
Kazalika, kundin ya nuna cewa, an yi asarar megawatts da ta kai 149,524, wanda hakan ya nuna cewa, an tabka asarar da ta kai ta Naira biliyan 2.38 s 2022, inda adadin ya karu zuwa kashi 164.7 ya kuma kai Naira biliyan 6.3, a 2023, saboda asarar da aka yi ta megawatts 229,370 a duk sa’a daya.
A cikin watannin sha daya na 2024,adadin ya karu zuwa kashi 247.14 ko kuma na Naira biliyan 15.57, zuwa Naira biliyan 21.87, saboda a asarar da aka yi ta makamashi da ta kai ta megawatts 356,759 megawatts a duk sa’a daya.
Wasu karin matsalolin da tashoshin ke fuskanta su ne, na yayanyi, kuskuren ‘yan Adama, rashin daukar matakai a kan lokaci, yawan yi na’urorin lodin wuta, rashin bai wa na’urorin kulawar ta ta kamata da lalacewar kayan aiki wanda hakan ya sanya kafanonin rabar da wutar na GenCos suke yin asarar samun kudaden shiga.