Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai kOya muku yadda ake danwaken zamani.
- Trump Ya Gayyaci Mark Zuckerberg Cin Abinci
- Sergio Mattarella: Duk Matakan Da Ke Rungumar Hadin Gwiwa Dukiyoyi Ne Masu Kima Na Kasashen Duniya
Ga dai abubuwan da za ku tanada:
Filawa, Kuka, Kanwa, Yaji, Mai, Kabaiji, Tumatur, Kokumba, Kwai, Albasa,
Yadda za ku hada:
Idan kuka samu kanwa sai ku zuba a bokiti ko kuma wani abu mai zurfi, sannan ku zuba ruwa mai yawa yadda zai isa kwabin danwaken, sannan ku samu ruba ku zuba filawarku daidai yadda za ta ishe ku, sannan ku zuba kuka ita ma daidai yadda za ta ishi filawar idan kuna so ana dan zuba gishiri kadan haka, sannan ku gauraya su sai ku zuba ruwan kanwar da kuka jika ku kwaba shi yadda dai ake kwabin danwake ku dora ruwa idan ya tafasa sai ku jefa idan ya dahu sai ku kwashe, bayan kun kwashe, sannan sai ku samu kabajinku ku yayyanka shi ku wanke ku ajiye a gefe, sai tumatur shima ku wanke ku yayyanka ku ajiye a gefe, haka albasa, kokumba itama ku wanke ku yayyankata, amma da kabajin da kokumba kusa musa dan gishiri wajen wankewar, sai ku dafa kwan, ku bare shi.
Idan kuka zuba dan waken a kwanon da za ku ci sai ku zuba Mai wanda dama kun soya shi da albasa sai ku zuba kabaji da kokumba da tumatur da albasa sai ku yayyanka kwan a kai ku ci tare da su. Yana da dadi sosai.