Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi tir da yadda Arewacin Nijeriya ta kasa amfani da yawan al’ummarta wajen ci gaba, yana mai cewa masu ruwa da tsaki ya kamata su mayar da hankali wajen zuba jari a fannonin ilimi da noma domin haɓaka yankin.
A yayin da yake magana a matsayin mai jawabi a bikin murnar shekara 50 na ziyarar Sheikh Ibrahim Nyass, wanda ya kafa Faidha Tijjaniyya a Yammacin Afrika, a Jos, Jihar Filato, Sarki Sanusi II ya nuna cewa mafi yawan al’ummar Arewa na dogaro da noma ne wajen dogara da kai, ba tare da samun damar amfani da sabbin fasahohi a noma ba.
- Shugabancin Nijeriya: ‘Yan Arewa Ku Jira Har Zuwa 2031 —Sakataren Gwamnatin Tarayya
- Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II
Ya bayyana cewa dole ne Arewa ta sabunta hanyoyin nomanta da inganta tsarin ilimi domin fita daga wannan koma bayan da ke addabar yankin.
A cikin jawabin da ya yi mai taken ‘Muhimmancin Rayuwa Tare a Tsarin Al’adu da Addinai’, Sarki Sanusi II ya kawo misalan tarihi na zaman lafiya, inda ya ambaci ziyarar Sheikh Ibrahim Nyass Nijeriya shekaru 50 da suka wuce domin yaɗa zaman lafiya tsakanin Musulmai da waɗanda ba Musulmai ba a Jihar Benue-Filato na lokacin.