Cinikayyar waje ta hajojin kasar Sin ta bunkasa da kaso 10.4 bisa dari cikin watanni 7 na bana, inda darajar kudaden cinikayyar ya kai kudin Sin tiriliyan 23.6, wato kimanin dalar Amurka tiriliyan 3.5 ke nan.
Hukumar kwastam ta kasar, ta ce mizanin kayayyakin da kasar ke fitarwa ya karu da kaso 14.7 bisa dari a shekara, zuwa yuan tiriliyan 13.37, yayin da na hajojin da ake shigowa da su ya karu da kaso 5.3 bisa dari a shekara, zuwa yuan tiriliyan 10.23.
Alkaluman hukumar ta kwastam sun nuna cewa, cinikayyar Sin da gamayyar kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya, ta karu da kaso 13.2, kana ta Sin da tarayyar turai ta karu da kaso 8.9 bisa dari, yayin da ta Sin da Amurka ta karu da kaso 11.8 bisa dari cikin shekara guda.
A daya hannun kuma, tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, cinikayyar Sin da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya ta karu da kaso 19.8 bisa dari, yayin da ta Sin da kasashen dake cikin gamayyar hadin gwiwar raya tattalin arziki ta RCEP, ta karu da kaso 7.5 bisa dari a shekara.
Da yake tsokaci game da hakan, kakakin hukumar kwastam ta kasar Sin Li Kuiwen, ya ce a watan Yuli, cinikayyar Sin da kasashen dake cikin gamayyar hadin gwiwar raya tattalin arziki ta RCEP, ta kai darajar yuan tiriliyan 1.17, wato karuwar kaso 18.8 bisa dari a shekara guda, wanda kuma hakan ya bunkasa daukacin sassan cinikayyar waje da Sin ke gudanarwa, da kaso 5.6 bisa dari. (Saminu Alhassan)