A bana, masu yawon shakatawa da suka zo kasar Sin daga ketare sun karu da kaso mai yawa. A ranar 17 ga wannan wata, kasar Sin ta sanar da kara sassauta manufarta ta yada zangon matafiya ba tare da biza ba, lamarin da ya jawo hankalin al’ummun kasa da kasa matuka bisa alkaluman da aka samar.
Tun daga watan Yulin shekarar bara, kasar Sin ta fara yin kokarin kyautata manufar yada zango ba tare da biza ba. Kawo yanzu, kasar Sin ta riga ta daddale yarjejeniyar shiga kasa ba tare da biza ba daga duk fannoni da kasashe 26, tana aiwatar da manufar shiga kasa ba tare da biza ba ta bai daya da kasashe 38, ciki har da Faransa da Jamus, kuma ta daddale yarjejeniyar yada zango ba tare da biza ba da kasashe 54. Ban da haka, ta daddale yarjejeniyar shiga kasa ba tare da biza a tsakanin juna ba da kasashe 157 a fadin duniya. Ana iya cewa, tsarin biza ya nuna kokarin da kasar Sin take yi wajen kara habaka bude kofa ga ketare.
Har yanzu da sauran rina a kaba yayin bude kofa ga juna tsakanin kasa da kasa, amma manufar bude kofa a matsayin koli ga ketare da kasar Sin ke aiwatarwa ta ingiza cudanyar al’umma da kudade da kayayyaki a tsakanin kasa da kasa.
Nuna halin kirki da soyayya ga baki al’adar al’ummar Sinawa ce, haka nan bude kofa da yin hakuri ga saura ta kasance hanyar yin cudanya da kasashen duniya ta kasar Sin. Kasar Sin tana maraba da zuwan abokan ketare yankunanta domin su kara fahimtar yanayin da take ciki, tare kuma da cin gajiyar bunkasarta. (Mai fassara: Jamila)