Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin ta karbo rancen dala biliyan daya domin tallafa wa aikin matatar man Dangote a lokacin da ta fuskanci wasu matsaloli na kudi.
Babban jami’in yada labarai na kamfanin NNPC, Olufemi Soneye, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan harkokin makamashi a Abuja.
- Kasar Sin Na Adawa Da Danne Kamfanoninta Da Amurka Take Yi Bisa Fakewa Da Batun Tsaron Kasa
- Shugaban Sin Ya Jinjinawa Nasarorin Da Yankin Macao Ya Samu Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata
Da yake karin haske kan nasarorin da babban kamfanin mai na kasa a karkashin jagorancin Malam Mele Kyari ya samu, Sonoye ya ce, “ A karkashin jagorancin Mele Kyari mai hangen nesa, kamfanin NNPC Ltd ya samu nasarori masu ywa, inda ya sake fayyace yadda harkar man fetur da iskar gas ta Nijeriya ke tafiya.
“Sake bude matatar man ta Fatakwal ya nuna wani gagarumin sauyi a yunkurin Nijeriya na samun wadatar makamashi, yana mai jaddada aniyar kamfanin na farfado da aikin tace man fetur a kasar nan.
“Haka zalika, NNPC ta yi nasarar daukar iskar Gas (CNG) a matsayin wata hanyar samar da makamashi, wanda zai bai wa ‘yan Nijeriya mafita a cikin tsadar makamashi a duniya.
“Shawarwari mai muhimmanci na samun lamunin dala biliyan 1 da NNPC ta goyi bayan ya taka rawar gani wajen tallafa wa matatar man Dangote a lokacin da ake fama da matsalar rashin mai, wanda ya bayar da hanyar samar da kafa matatar mai ta farko mai zaman kanta a Nijeriya. Wannan yunkurin ya nuna himma da kwazon kamfanin na NNPC na habaka hadin gwiwar jama’a da masu zaman kansu wadanda ke haifar da ci gaban kasa.
“A wata nasara mai cike da tarihi, NNPC, a karkashin jagorancin Kyari, ta bayyana riba a karon farko cikin shekaru da dama, wanda ke nuna gagarumin sauyin kudi. Tuni dai kamfanin ya zarce hasashen ribar da yake samu a shekarar 2024, lamarin da ke nuni da sauye-sauyen da ya aiwatar.
“Bugu da kari, Kyari ya saukake rancen dala biliyan 3 na Gazelle, wani muhimmin tsoma bakin da ya taimaka wajen daidaita al’amuran tarayya a lokacin da ake fama da matsalar canjin kudin waje,” in ji shi.