Shugaban kasar Sin Jinping, a yau Juma’a, ya jinjina wa sauye-sauye masu ma’ana da aka samu a yankin Macao tun daga lokacin da ya dawo kasarsa ta asali ta Sin a shekarar 1999.
Xi ya bayyana cewa, an samu gagarumar nasara wajen “aiwatar da tsarin mulki biyu a cikin kasa daya” bisa halin musamman na yankin Macao.
- Yayin Da Ake Gab Da Bukukuwan Kirsimeti: ‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Rayuwa Cikin Matsin Tattalin Arziki
- Yadda Ciniki Ya Habaka Tsakanin Babban Yankin Kasar Sin Da Yankin Macao A Fiye Da Shekaru 25
Shugaba Xi ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a bikin cika shekaru 25 da dawowar yankin musamman na Macao kasarsa ta asali ta Sin da kuma rantsar da gwamnatin yankin Macao na musamman a wani sabon wa’adin mulki na shekaru shida.
Xi ya kuma yi kira ga sabuwar gwamnatin yankin na musamman ta habaka tattalin arzikin cikin gida, da kyautata shugabanci, da samar da wani dandali na tsarin bude kofa mai iganci da kuma kiyaye walwalar jama’a da kwanciyar hankali.
Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, tabbas yankin Macao zai samar da sabbin sararin kawo ci gaba da kirkiro da sabbin hanyoyin samun albarka matukar an ci gaba da cikakkiyar aiwatar da manufar “aiwatar da tsarin mulki biyu a cikin kasa daya” daidai-wa-daida ba tare da wata tangarda ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)