Wata mata da hukumar hana sha da fataucin kwayoyi NDLEA ta cafke, ta bayyana cewa ta tsunduma cikin harkar ne don tara kudin fansa naira Miliyan N5m domin kubutar da mahaifiyarta daga hannun ‘yan bindiga.
Jami’an hukumar NDLEA sun kama Matar ce mai suna Jatau Lydia Lami a filin jirgin sama na Legas bisa kokarin fitar da Tramadol 225mg guda 1,700 da aka boye a cikin jakunkunanta zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya ta jirgin Turkish Airline ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli, 2022.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wacce ake zargin, mai ‘ya’ya uku, ‘yar asalin karamar hukumar Zango Kataf ce ta jihar Kaduna kuma tana zaune a birnin Istanbul na kasar Turkiyya tare da iyalanta.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya sanyawa hannu, ya ce Matar ta tsunduma harkar kwayar ne da nufin tara kudaden fansar mahaifiyarta naira miliyan 5 daga hannun ‘yan bindiga, wadanda suka yi garkuwa da ita tun watan Yuni, 2022.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp