An yi bikin nuna fina-finai da shirye-shiryen telabijin na Habasha da Sin, jiya Asabar, a birnin Adis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.
A cikin jawabin da ya yi a wajen bikin, Chen Hai, jakadan kasar Sin a kasar Habasha, ya ce dukkan kasashen 2 wato Habasha da Sin, suna da dogon tarihi da dimbin al’adu masu muhimmanci, wadanda suka samar da albarkatu ga ci gaban harkokin yada labarai ta kafofin rediyo da telabijin, da tsara fina-finai da shirye-shiryen telabijin masu kyan gani. Ban da haka, a shekarun baya bayan nan, kasashen 2 na kokarin cudanya da hadin gwiwa da juna, ta fuskar daukar fina-finai da shirye-shiryen telabijin, inda suke samun dimbin nasarori.
Haka kuma wajen bikin, an nuna fim din labarin gaske mai taken ” The Road to Prosperity” wato “Hanyar Zuwa Ga Samun Wadata “, da babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya samar, wanda ya samu karbuwa sosai a wajen masu kallo. (Bello Wang)