Arsenal ta fuskanci babban ƙalubale bayan da aka tabbatar Bukayo Saka ya samu rauni a ranar Litinin, Mikel Arteta ne ya tabbatar da cewa ɗan wasan gefe Bukayo Saka zai yi jinyar makonni saboda raunin da ya samu.
Saka ya samu raunin ne a farkon mintuna 45 na wasan da Arsenal ta doke Crystal Palace da ci 5-1, inda Leandro Trossard ya maye gurbinsa.
- Arsenal Ta Yi Barin Maki A San Siro
- Arsenal Da West Ham Sun Kafa Tarihi A Wasan Da Suka Tashi 5-2 A London
A ranar Juma’a ne Arsenal za ta kece raini da Ipswich Town a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Kirsimeti a fadin Duniya.
Arsenal na fatan lashe gasar Firimiya a wannan karon bayan ta barar da damarta sau biyu a cikin shekaru uku inda Manchester City ta lashe duka kofunan biyu.