Wani mutum a Jihar Ebonyi, mai suna Joshua Nwafor, ya kashe matarsa mai sun Charity, bayan da taƙaddama a kan doya ta ɓarke a tsakaninsu.
Lamarin ya faru ne bayan ma’auratan da suka kwashe shekaru 17 da aure, suka samu sabani a kan yadda za a sarrafa doyar.
- Tabbas Manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu” Za Ta Yi Karko Ta Samu Ci Gaba
- Masu Amfani Da Wayar Salula Ta 5G A Kasar Sin Sun Kai Fiye Da Biliyan 1
Charity, ta fi son a soya doyar, yayin da Joshua ke son a dafa ta.
Ce-ce-ku-cen ya ƙara zafi, har Joshua ya kulle matarsa a ɗaki sannan ya yi mata dukan kawo wuƙa har ta mutu.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Joshua Ukandu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da an gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.