Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatinsa ga sauye-sauyen haraji, inda ya ce suna da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziƙin Nijeriya.
A yayin taron manema labarai na farko da ya gudanar a Legas, Tinubu ya bayyana cewa sauye-sauyen haraji suna nufin inganta tsarin haraji, faɗaɗa tushen kudaden shiga, da kuma tallafawa ci gaban ƙasa.
- Ban Taɓa Nadamar Cire Tallafin Man Fetur Ba – Tinubu
- Tinubu Zai Tattauna Da Kafafen Yaɗa Labarai A Karon Farko Yau
“Sauye-sauyen haraji za su dore,” in ji Tinubu.
“Ba za mu iya sake bunƙasa tattalin arzikinmu da tsofaffin hanyoyi ba.”
Ya bayyana cewa sauye-sauyen suna nufin faɗaɗa tsarin haraji ba tare da cutar da masu karamin ƙarfi ba.
Shugaban ƙasar ya kuma jaddada buƙatar kawar da haraji na zamanin mulkin mallaka da magance ƙim biyan haraji, inda ya yi kira da inganta da sabunta tsarin.
Tinubu ya kare aikin ministocinsa duk da suka da suke fuskanci, inda ya ce ministocinsa suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya su karbi sauye-sauyen haraji a matsayin wani abu mai muhimmanci don samun ci gaba.
“Manufar sauye-sauyen haraji shi ne bunƙasa da ci gaba. Sabuwar rana ta shigo, kuma na yi imanin da hakan,” in ji Tinubu.