Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta bayyana aniyarta ta kara yawan kudaden da za ta kashe, da kuma bayar da lamunin gwamnati a shekarar 2025 domin samar da tallafi mai karfi da zai karfafa dora tattalin arziki a kyakkyawar turba.
Bugu da kari, kasar Sin za ta kuma yi amfani da tsarin manufar kashe kudi mai inganci a shekara mai kamawa, tare da tabbatar da cewa manufofin kudi na ci gaba da yin karfi da tasirin da ake bukata, kamar yadda ministan kudi Lan Fo’an ya bayyana, a yayin gudanar da babban taro kan tsara ayyukan manufofin kudi na kasa na kwanaki biyu da aka kammala a yau Talata.
Manufar kashe kudaden na gwamnati dai ta zo dai-dai da sanarwar da aka bayar kwanan baya game da alkiblar da aka ce za a dosa, a taron tattaunawa kan aikin tattalin arziki na kwamitin kolin JKS. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)