Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana a jiya Litinin cewa, a wannan rana, ofishin wakilin kasuwanci na Amurka, ya sanar da gudanar da bincike bisa aya ta 301 ta dokar ciniki da takara ta 1988 ta kasar, kan manufofin sana’o’in na’urorin lantarki na kasar Sin, sai dai kuma a bangarenta Sin na matukar adawa da hakan.
Wannan jami’in ya ce, binciken mataki ne na kare kai sama da kima, da baiwa kasuwa kariya. Tuni dai WTO ta yanke hukuncin cewa, karin harajin da Amurka ke dorawa kasar Sin karkashin aya ta 301 ya sabawa ka’idojin WTO, kuma mambobin kungiyar ba su amince da hakan ba. Kaza lika kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta sau da dama.
- An Kaddamar Da Manyan Masana’antu 8 Masu Jarin Kasar Sin A Uganda
- Canada Za Ta Caka Wa Kanta Wuka Kan Matakin Da Ta Dauka A Kan Kasar Sin
Bugu da kari, Amurka ta aiwatar da sabon bincike kan sana’o’i masu alaka da na’urorin lantarki ne don dakile kasar Sin, bisa burinta na siyasa, duk da hakan zai illata tsarin samar da na’urorin lantarki na duniya, da rusa moriyar kamfanoni da Amurkawa masu sayayya.
Ma’aikatar kasuwancin kasar Amurka, ta fitar da wani rahoto a kwanakin baya, wanda ke cewa yawan na’urorin lantarkin da Amurka ta shigo da su daga kasar Sin, sun kai kashi 1.3% kacal na dukkan na’urorin lantarki a kasuwannin Amurka. Kana yawan irin wadannan hajojin da Sin ta fitar zuwa Amurka bai kai wadanda ta shigo da su daga Amurka ba.
Kasar Sin na kalubalantar Amurka, da ta mutunta gaskiya, da ka’idar gudanar da harkoki tsakanin kasa da kasa, ta dakatar da matakanta na kuskure. Har ila yau, Sin za ta ci gaba zura ido kan wannan bincike, da daukar kowane mataki na wajibi, don kare halalttaccen iko da moriyarta. (Amina Xu)