Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano, ta kama wasu mutane 34 da ake zargi da sayarwa da ta’ammuli da miyagun kwayoyi daban-daban a jihar.
Kakakin Hukumar, ASN Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.
- Nijeriya Ba Ta Cikin Kasashe 10 Da Suka Fi Cin Bashi A Afirka – IMF
- Gwamnatin Tarayya Ta Wanke Mutane 888 Daga Zargin Ta’addanci
Muhammad-Maigatari ya rahoto kwamandan hukumar na jihar, Abubakar Idris-Ahmad, yana cewa, an kama wadanda ake zargin ne a yayin wani samame da aka kai, a wani mataki na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Wuraren da aka kai samamen sun hada da Unguwar Fagge, da filin wasa na Sani Abacha, da Danagundi, da kuma Filin Idi.
Ya ce rundunar ta samu nasarar kwace wasu haramtattun kwayoyi kamar su tabar wiwi, ‘suck and die, da kuma ‘Exol-5’ da dai sauransu.
Sauran kayayyakin da aka kwato a cewarsa, sun hada da, makamai masu hatsarin gaske da masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi ke amfani da su wajen kai wa jami’ai hari.