Rahotanni sun bayyana cewa, ana fargabar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama sakamakon wani hari da jirgin yakin sojojin Nijeriya ya kai wa ‘yan ta’addar Lakurawa a maboyarsu, inda ya yi kuskuren jefa bama-bamai a wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Silame ta jihar Sakkwato.
Al’ummomin da abin ya shafa, a cewar wata majiya daga cikin al’ummar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Laraba, a kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa.
- Yadda Fasahar Sadarwa Ta Bunkasa A Kasar Sin Zuwa Karshen 2024
- Sanata Barau Ya Roƙi Ganduje Ya Ƙwato Jihohin Da Suka Yi Wa Jam’iyyar APC Tutsu
Shima da yake tabbatar da harin, shugaban karamar hukumar Silame, Alhaji Abubakar Muhammad, ya ce tawagarsa na ci gaba da tantance irin barnar da harin ya haifar.
“Mutanen kauyen suna zaune lami lafiya a lokacin da bama-bamai suka fara fado wa al’ummar.
“Amma ya zuwa yanzu, ba za a iya tabbatar da adadin mutanen da aka kashe ko kuma suka jikkata ba saboda har yanzu muna kan tantance mutanen da lamarin ya shafa,” in ji shi.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ki cewa komai kan faruwar lamarin, inda ya ce ba aikin ‘yansanda ba ne.
Haka zalika, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) a jihar ta cutura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.