Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Fansar Yamma da ke aiki a Arewa maso yamma sun tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda da dama a kusa da tsaunin Bichi a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Sojojin tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da raunata wasu manyan kwamandojinsu, Manore da Dogo Nahalle a farmakin.
- Amurka Da Phillippines Sun Hada Karfi Don Kalubalantar Sin Kan Batun Tekun Kudancinta
- Sojoji Sun Kama Mutane 20 Kan Zargin Kashe-kashe A Jihar Filato
Mai magana da yawun rundunar, Lt-Col. Abubakar Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kai farmakin ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka bayyana ayyukan ta’addanci a yankin, wanda ya kai ga hare-hare a kananan hukumomin Danmusa, Safana, da Kankara na jihar a ranar 19 ga watan Disamba. , 2024.
Ya ce, sojojin na kasa da na sama sun kai harin ne kan sansanonin da aka gano a kokarinsu na wargaza ayyukan ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da ke fama da ayyukan ta’addanci.
Ya ce hare-haren sun yi sanadiyyar kashe ‘yan ta’adda da dama, ciki har da raunata wasu fitattun kwamandojinsu, Manore da Dogo Nahalle.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp