Dakarun haɗin gwiwa na rundunar soja ta “Operation Safe Haven” (OPSH), ta ce ta yi nasarar kama wasu mutane 20 da ake zargi da hannu a kashe-kashen da aka yi a ƙauyen Tingwa Gidan Ado, da ke ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato.
Babban kwamandan rundunar Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan a yayin liyafar cin abincin Kirsimeti da aka shirya wa sojoji ranar Alhamis a Jos.
Janar Abdulsalam, wanda kuma shi ne babban kwamandan runduna ta 3 na sojojin kasan Nijeriya, ya ce dakarunsu sun kuma ƙwato tarin makamai da alburusai da sauran muggan makamai.
Kwamandan ya yabawa dakarun na OPSH, da na runduna ta 3 bisa sadaukarwar da suke bayar wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da ake samu a jihar musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Ya godewa babban hafsan tsaron kasa (CDS),
Janar Christopher Musa, da Laftanar Janar Olufumi Oloyede, Babban Hafsan Sojoji (COAS), na jagorancinsu da taimaka wa sojoji don samun nasara a yaƙar ta’addanci da suke.
Idan za a iya tunawa, a ranar 22 ga watan Disamba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Tingbwa Gidan Ado, da ke ƙaramar hukumar Riyom, a jihar Filato inda suka kashe mutane 15 tare da jiggata wasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp