Wani jirgin saman Jeju Air dauke da fasinjoji 181 daga kasar Thailand zuwa Koriya ta Kudu ya yi hatsari a lokacin da ya isa filin jirgin sama na kasar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya afkawa wata katanga daga bisani kuma wuta ta tashi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar duk wanda ke cikin jirgin sai dai mutum biyu da suka tsira da aka ciro daga cikin tarkacen jirgin.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa, akwai yiwuwar tsuntsaye ne suka haddasa hatsarin – bala’in da ba a taba-taba gani ba a kasar Koriya ta Kudu – wanda kusan fasinjoji duka suka kone tare da jirgin, a cewar jami’an kashe gobara.
- Wata Gidauniyar Kasar Sin Ta Mika Ma’ajiyar Ruwa Ga Al’ummar Wani Kauyen Habasha
- Bunkasar Tattalin Arzikin Sin Ta Kawo Damammaki Ga Duniya
Bidiyon ya nuna yadda Jeju Air Boeing 737-800 ya sauka ta cikinsa a filin jirgin sama na Muan, daga bisani sai hayaki ya fara fitowa daga injinan, sannan ya yi bindiga da wuta.
“Daga cikin fasinjoji 179 da suka mutu, an iya gano 65,” in ji hukumar kashe gobara ta kasar, inda ta kara da cewa, sauran tuni aka fara binciken kwayoyin halittarsu don fayyace hakikaninsu tare da sunansu.