Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da jawabin taya murnar shigowar sabuwar shekarar 2025 da karfe 7 na yammacin ranar Talata, bisa agogon Beijing.
Manyan gidajen talabijin da rediyo na rukunin gidajen talabijin da rediyo na kasar Sin wato CMG, da shafukansu na yanar gizo, da sauran sabbin kafofin watsa labarai na manyan kamfanonin dillancin labarai na kasar Sin, da suka hada da jaridar People’s Daily da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da dai sauransu, za su watsa bayanin jawabin. (Mohammed Yahaya)