Kasar Sin ta sabunta jadawalin sufurinta na jiragen kasa a fadin kasar tare da kara yawan daruruwan jiragen fasinja da masu dakon kaya a cikin layukanta na dogo da take da su.
Sauye-sauyen da aka samu da suka fara aiki a jiya Lahadi da dare, na da nufin inganta jin dadin fasinjoji ne, da habaka dakon kayayyaki da kuma kara hade hancin harkokin tattalin arzikin manyan yankuna.
Sabon jadawalin da aka yi ya kunshi shigar da karin jiragen kasa na fasinja guda 230 wanda ya mayar da jimillarsu zuwa 13,028, da kara yawan jiragen dakon kaya 91 wadda ita ma jimillarsu ta karu zuwa 22,859.
Harkokin sufurin jiragen kasa a tsakanin iyakoki na Guangzhou zuwa Shenzhen zuwa Hong Kong a layin jirgin kasa mai sauri, sun samu gagarumin ci gaba inda adadin zirga-zirgar jirgin mai sauri a tsakanin iyakokin ya karu zuwa 242.
Kazalika, a karon farko, za a samu zirga-zirgar jiragen kasa kai-tsaye a tsakanin tashar jirgin kasa ta Kowloon da ke yankin Hong Kong ta Yamma da kuma babban yankin kasar Sin ta shiyyar yammaci da arewacinta, inda hakan zai kara saukaka tafiye-tafiye da hada-hadar kasuwanci a tsakanin babban yankin kasar Sin da na Hong Kong. (Abdulrazaq Yahuza Jere).